d73207dd44bbca1e0c329da9425975a4.jpg
a4d0e7efe918b6a7978544d42ab9d86f.jpg
dc59823d0f7293b2b8e392f84a335c2a.jpg

Hausa Rigar Siliki

 

GidanHausa.com babban shafin intanet ne a harshen Hausa, irinsa na farko da aka kirkira wanda ya kunshi:

  • Nishadantarwa, 
  • Zumunta 
  • sadarwa, 
  • Tarihi, 
  • Ilimantarwa, 
  • Fadakarwa da dai sauransu

Wannan babban shafi zai zamo wani gida ne na al’ummar Hausawa da masu sha’awar wannan harshe na Hausa mai ‘dimbin daraja da albarka, inda zaku iya samun duk wani abu da ya danganchi Hausa da al’adun Hausawa. 

Haka kuma ya zamo wata mahadar al’ummar Hausa – Fulani, a duk inda suke a duniya, domin chi gaba da ya’da al’adunmu tare da kyawawan ‘dabi’unmu ga sauran al’ummomin duniya baki ‘daya.  Kazalika wannan gida zai zamo garabasa ko kuma wata hanya mafi sauki ga ‘yan baya da basu rabauta da rayuwa da zamantakewar iyaye da kakanni ba, tare da samun tarihi irin na kunne ya girmi kaka.

Ina al’ummar Hausa-Fulani na duniya baki d’aya ga abu namu maganin a kwab’e mu. K’ofar mu a bud’e take ga duk wanda yake da sha’awar bada gudumawarsa wajen bunk’asar wannan gida, da yazo ya bayar. Haka kuma duk wanda Allah ya huwachewa wata fikira ko ilhamar da za ta amfanawa wannan al’uma tamu, shima muna maraba da shi. 

Kada fa ku manta Hausawa na chewa ‘’kowa ya bar gida…’’ Haka kuma ana cewa  “HAUSA RIGAR SILIKI”